Kididdiga ta rage yawan halittun ruwa

Ruwan teku Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ruwan teku

ekuAna gab da kammala wani gagarumin kokari na kididdige adadin halittun ruwa.

Ya dauki kwararru masana halittun ruwa tsawon shekaru takwas su tattara bayanai da hada yawan abinda aka kira Rajistar halittun ruwa na duniya.

Daga cikin nau'oin halittun ruwan 419,000 da aka yi lissafi a kimiyya kimanin rabi na (190,400) an nuna su ne sau biyu a jerin halittun.

Wasu nau'oin na dodon-kodi na teku suna da sunaye dabam-dabam har 113.

Editoci sun ce adadin nau'oin halittun ruwan a yanzu yan kan 228,450.

Mafi rinjayensu - watau kashi 86 bisa dari da halittun ruwan kimanin 195.000 dabbobi ne.

Wannan ya hada da nau'oin kifaye sama da 18,000 da aka bayyana tun tsakiyar shekarun 1700, fiye da 1,800 na taurarin teku da kifin whale 93 da dolphines da kuma wasu nau'oin na kifayen Clams 8,900.

Sauran jerin namun ruwan sun hada da sauran tsirrai na teku da shukoki da cututtuka da wasu halittun na ruwa.

Kodayake an zaftare yawansu a lokacinda ake tattara bayanai, amma adadin ya cigaba da karuwa.

A shekara ta 2014, an kara adadin wasu sabbin halittun ruwan 1,451 a rajistar.

An yi kiyasin wasu nau'oi na halittun ruwan 10,000 ko fiye da haka suna dakunan bincike a sassa dabam-dabam na duniya, suna jiran a gabatar da bayanai a kan su.

Karin bayani