Saudiyya ba ta son Iran ta mallaki nukiliya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Irana ta ce shirinta na zaman lafiya ne

Wani babban jami'i a masarautar Saudiyya ya yi gargadin cewa yarjejeniyar domin bai wa Iran damar ci gaba da shirinta na nukiliya za ta bai wa wasu kasashe a yankin damar fara kera nasu makaman kare dangin.

Prince Turki al-Faisal ya shaidawa BBC cewa, Saudi Arabia ma za ta iya bukatar bata irin wannan damar kamar sauran kasashe.

Ya ce " Duk matsayar da aka cimma a wadannan tattaunawar, muma za mu bukaci a bamu irin ta. A saboda haka idan har Iran za ta samu damar kera makamashin Uranium, ba wai Saudi Arabia ce kadai za ta bukaci wannan damar ba,sauran kasashen duniya ma za su so wannan damar."

Manyan kasashen duniya shida na ci gaba da tattaunawa da Iran a kan batun takaita ayyukanta na inganta makamashin uranium.

Sai dai kuma wannan tattaunawa na samun suka akan cewa yakamata shirin Iran na nukiliya ya zo karshe.