Za a mayar wa Nigeria dala miliyan 380 na Abacha

Image caption Margayi Abacha ya mulki Nigeria na tsawon shekaru biyar

Babban Lauyar gwamnatin Switzerland za ta mayar wa Nigeria kusan dala miliyan 380 mallakar tsohon shugaban mulkin soji, Janar Sani Abacha.

Abacha wanda ya mulki Nigeria tun daga shekarar 1993 ya rasu a kan karagar mulki a shekarar 1998.

A cikin watan Yulin 2014, aka cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Nigeria da iyalan Janar Abacha kan batun maidoda wasu daga cikin kudin da Abacha ya mallaka a Switzerland.

A cikin yarjejeniyar, idan aka maido wa Nigeria kudaden za ta janye shari'ar da ta ke yi tsakaninta da Abba Abacha, da ga Janar Abacha.

Tun a shekarar 1999, aka soma batun kudaden da ake zargin Janar Abacha ya sace inda kuma kawo yanzu hukumomi a Switzerland suka taimaka aka mayar wa gwamnatin Nigeria kusan dala biliyan biyu da miliya dubu dari biyu.