An yanke wa Mohammed Badie hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Badie dai ya yi ta fuskantar shari'oi da dama a kasar.

Wata kotu a Masar ta yanke wa jagoran kungiyar 'yan uwa Musulmi, Mohammed Badie hukuncin kisa tare da wasu fitattun 'yan kungiyar su 13.

Kotun ta ce an samu dukkanin mutanen 14 da laifin shirye-shiryen kai wa gwamnatin kasar hari.

Mr Badie dai ya yi ta fuskantar shari'oi da dama a kasar.

An yanke masa hukuncin kisa tun ma kafin wannan shari'ar a wasu shari'un da aka yi masa, amma daga bisani aka rage hukuncin zuwa daurin rai da rai.

An ayyana kungiyar 'Yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar 'yan ta'adda a shekarar 2013.

A ranar 11 ga watan Aprilu ne za a yi zaman karshe na sauraron karar, duk da cewa masu laifin za su iya daukaka kara.