Kotun ICC ta gargadi 'yan siyasar Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption Jam'iyyar PDP na fuskantar babban kalubale daga jam'iyyar APC

Kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya, ICC ta gargadi 'yan siyasar Nigeria da su guji yin duk wasu abubuwa da za su kai ga tayar da hankali gabani da kuma bayan zabukan kasar.

A wata sanarwa da babbar mai shigar da kara ta kotun, Fatou Bensouda, ta fitar ta jaddada cewa duk wani mutum da aka samu yana furta kalamai ko tayar da hankali, ko kuma bayar da goyon baya aka aikata haka, kotun za ta hukunta shi.

Dukkanin manyan jam'iyyun biyu dai wato PDP mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta APC, sun shaida wa BBC cewa ba za su yi duk wani abu da zai tayar da hankula ba.

A baya dai jam'iyyun biyu sun zargi juna da yin abubuwa da kuma kalamai na tayar da hankula.

Wani lamari na baya bayan nan shi ne zargin da jam'iyyar APC ta yi wa uwargidan shugaban kasa, Patience Jonathan da yin kalamai na tayar da rikici inda ta yi kira da a jefi masu neman canji.

Sai dai wani mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Shugaba Jonathan ya ce uwargidan shugaban kasar za ta iya yin kuskure a matsayin ta na dan-adam.

A ranar 28 ga watan Maris ne za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na 'yan majalisun dokoki.