Ana zaben 'yan majalisar dokoki a Isra'ila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daga Yitzhak Herzog har Benyamin Netanyahu sun gargadi masu zabe da kada su zabi gamayyar da dayan ke jagoranta.

A ranar Talata ne jama'a a Israila ke zabukan 'yan majalisar dokoki, inda Firayi Minista Benjamin Netanyahu yake burin zama shugaban da ya fi kowanne jimawa a kan mulkin kasar.

Amma jam'iyyarsa ta Likud na biye ne da gamayyar jam'iyyun adawa a kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka gudanar, kuma ana tsammanin za a fafata sosai fiye da yadda ake zato.

A yakin neman zabensa, Mr Netanyahu ya mayar da hankalali ne a kan tsaron kasa.

Sai dai Gamayyar jam'iyyun adawar ta zargeshi da amfani da tsaro wajen kawar da hankulan jama'a daga tarin matsalolin cikin gida irinsu tsadar rayuwa.

Wata mai rubuce- rubuce a shafin Intanet ta shaida wa BBC cewa ta yi imanin a wannan karon jama'a sun fi damuwa ne da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, irinsu hauhawar farashi, da karancin gidaje da kuma harkar ilmi.

Ita kuwa jam'iyar Zionist Union ta masu dan sassaucin ra'ayi, ta yi alkawarin kyautata dangantaka da Palasdinu da sauran kasashen duniya.