Jonathan ya gana da Jega da kuma jami'an tsaro

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana sa rai za a cimma matsaya a kan zaben

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da shugaban hukumar zaben kasar, Attahiru Jega, na ganawa da dukkan manyan jami'an tsaro na kasar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ana sa ran shugaban hukumar zaben zai yi musu bayani a kan shirye shiryen hukumarsa game da zabukan da ke tafe.

Kazalika ana sa rai manyan jami'an tsaron za su yi jawabi a kan nasarorin da suka samu game da yaki da 'yan Boko Haram da kuma shirye-shiryensu wajen ganin an yi zabe ba tare da matsalolin tsaro ba.

Rahotanni dai na cewa manyan jami'an gwamnatin kasar da dama na cikin mahalarta taron.

A ranar bakwai ga watan jiya ne hukumar zaben kasar ta dage zaben da aka shirya yi ranar 14 ga watan jiya bisa dalilan tsaro.

Ana sa rai za su fitar da matsaya a kan zaben na 2015.