Al'ummar Vanuatu sun koma shan ruwa mai gishiri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bala'i ya afkawa Vanuatu a makon da ya gabata

BBC ta gano cewa mutanen da ke rayuwa a tsibirin ihunka banza a kasar Vanuatu sun buge da shan ruwa mai dandanon gishiri a kokarin da suke na tsira da ransu bayan mahaukaciyar guguwar da ta afku a kasar makon da ya gabata.

Mazauna Mosso sun ce suna tsammanin zuwan masu kawo musu taimako daga kasashen waje.

Tuni kungiyoyin agaji suka fara kokarin gano yankunan da abin ya shafa wadanda ke wajen kasar.

Alice Clements ita ce mai kula da harkokin jin kai a asusun da kananan yara na majalisar dinkin duniya ta ce "a yanzu ko wacce irin gudunmuwa da mutane za su bayar ko kuma gwamnati, a zahirance za ta ceto rayukan mutane da dama."

Hukumomi na kokarin tuntubar wasu yankuna guda 65 na kasar bayan da mahaukaciyar iskar ta sa dubban mutane suka rasa gidajensu.