Illar rikicin Boko Haram akan noma

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sojoji sun kwato garin Baga

Bayanai na cewa rikicin Boko Haram da ya addabi Najeriya da wasu kasashe makwabtanta, ya kawo nakasu ga harkokin jama'a da dama.

Baya ga sanadiyar rasa daruruwan rayukan da daidaita dubbai, manyan abubuwan da rikicin yafi shafa su ne noma da kiwo da kuma kasuwanci, galibi a yankin arewa maso gabashin Najeriya inda wannan matsala ta fi kamari.

Duk da cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a fara wasu ayyuka na shirye-shiryen tunkarar damunar da ke tafe, wasu manoma da ke yankin sun ce ba za suyi noma ba kamar dai yadda ala'amarin yake shekarun biyun da suka gabata.

Wasu 'yan asalin garin Baga wadanda rikicin ya sanya suka yi gudun hijra zuwa wasu garuruwan sun ce duk da cewa an kwato garin nasu daga hannun 'yan Boko Haram ba za su iya koma wa garin ba ballanta har su yi shirin noma a bana.

Masana sun ce hakan ka iya yin tasiri kan rashin isasshen abinci a yankin.