Shayar da nonon uwa na kara basira

Image caption Shayar da nonon uwa na kara hazaka ga jarirai

Masu bincike sun ce wani nazari wanda ya dauki dogon lokaci da aka gudanar a Brazil ya nuna cewa jarirai wadanda aka shayar da su nono na tsawon lokaci suna zama masu basira da ilimi sannan kuma masu wadata.

Binciken wanda mujallar The Lancet Global Health ta wallafa, ya bi girman yara kanana ne zuwa har su zama manya sannan ya gano cewa manyan da aka shayar da su nono a lokacin suna jarirai har zuwa shekara guda sun fi wadanda aka shayar da su kasa da wata guda.

Ana tunanin cewa samun wasu sinadarai a cikin madarar nono da ke da mahimmanci ga ci gaban kwakwalwa ka iya bunkasa basira.

Masu binciken sun ce abubuwan da suka gano sun fi abubuwan da aka yi a baya saboda sun yi nazarin jarirai da dama a wani bangare na Brazil inda shayar da nonon uwa abu ne da ake ganin ana yi a shekaun 1980.