'An lalata galibin Masallatai a Afrika ta tsakiya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani Masallaci da aka rusa a Bangui

Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce an lalata galibin Masallatai a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, sakamakon rikicin da aka shafe na tsawo fiye da shekaru biyu.

Samantha Power, wadda ta ziyarci Jamhuriyar Afrika ta tsakiya a makon da ya gabata ta ce masallatai 19 ne kacal suka rage daga cikin fiye da 436 da ake da su a kasar.

An dai tafka rikici ne tsakanin Musulmai da Kiristoci.

Mrs Power ta bayyana damuwa a kan yadda lamarin tsaro zai kasance idan dakarun Faransa da na Tarayyar Turai suka fice daga kasar.

Rikicin kasar ya janyo mutuwar dubban mutane da kuma hasarar dimbin dukiya.