Ba mu ga 'yan matan Chibok ba - Minimah

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Minimah ya ce za a cigaba da kokarin gano inda 'yanmatan suke

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Kenneth Minimah, ya ce duk da sake kwato yankuna da dama da aka yi daga kungiyar Boko Haram, har yanzu ba a samu wata alamar da ke nuna musu inda 'yan matan Chibok suke ba.

Janar Minimah ya fadi hakan ne a ranar Talata, yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron majalisar tsaron kasar da aka yi a fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa.

"Ya zuwa yanzu babu wani labari, domin a duk yankunan da muka kwato mun yi bincike, amma gaskiyar magana ita ce lokacin da 'yan ta'adda ke arcewa sukan gudu tare da iyalansu," in ji Minimah.

Laftanar Janar Minimah ya kara da cewa "Amma muna fatan idan muka kara rutsa mayakan, kuma sauran yankunan suka kubuce musu za mu samu karin bayan kan wadannan 'yan matan."

Kalaman na Laftanal Janar Minimah na ci gaba da janyo martani daban-daban a cikin Nigeria, inda mutane da dama ciki har da iyayen yaran suka ce rundunar sojin kasar ta yi amai ta lashe ne a kan batun gano yaran.

"Ai wannan magana ba ta bamu mamaki ba, domin tun lokacin da aka sace yaran nan gwamnati kullum cikin karya take," in ji Dr Usman Emman Shehu, na kungiyar fafutukar ceto 'yan matan Chibok.

Sace 'yan matan Chibok ya jawo hankalin kasashen duniya da kungiyoyi wanda a yanzu za a jira a ga martanin da za su mayar a kan wannan batun.