Netanyahu ya lashe zaben Isra'ila

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Magoya bayan jam'iyyar Likud na murnar samun nasara

Benjamin Netanyahu ya samu nasara a zaben gama-gari da aka yi a Isra'ila.

Bayan an kamala kirga yawancin kuri'un da aka kada, jam'iyyar Likud ta samu kujeru 30 a yayinda jam'iyyar Zionist ke da kujeru 24.

Mr Netanyahu za iya kafa gwamnatin hadin gwiwa ba tare da wata matsala ba.

Kenan Netanyahu zai yi mulki wa'adi na hudu kuma hakan ya nuna yadda ya samu farin jini daga baya, duk da cewar kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a na farko ta nuna cewa zai iya fadi zabe.

A kwanakin karshe na yakin neman zabe, ya yi wa masu tsattsauran ra'ayi alkawarin cewar ba zai bari a samu kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta ba.

Wani babban jami'in Falasdinawa ya soki 'yan Isra'ila da suka zabi mamaya a maimakon tattaunawar zaman lafiya.