Isra'ila: Netanyahu zai lashe zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

Alamu na nuna cewa jam'iyyar Likud Party ta Firayi Ministan Israi'Ia Benyamin Netanyahu, tana gab da yin nasara a babban zaben da aka gudanar a kasar.

Yanzu haka jam'iyyar tana da kaso kusan 24 cikin dari na kuri'un da aka kada, sabanin 19 da jam'iyyar gamayya ta Zionist Union ta samu.

Tuni Mista Netanyahu ya jinjina wa jam'iyyar tasu, a inda yace nasarar ta samu ne sakamakon ayyukan alkairi da jam'iyyar ta mayar da hankali a kai.

Ya kuma kara da cewa zai mayar da hankali wajen kokarin cimma gwamnatin hadaka da kananan jam'iyyun kasar.