An kori mataimakin shugaban kasar Saliyo

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption A watan da ya gabata aka kori Samuel Sam Sumana daga jam'iyya mai mulki

Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya kori mataimakinsa daga kan mukaminsa bayan da ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Amurka.

A ranar Asabar din da ta gabata, Samuel Sam Sumana ya bayyana cewa ya tambayi jakadan Amurka a Saliyo cewa ya bashi inda zai fake saboda rayuwarsa na cikin hadari.

Tun farko sojoji sun kewaye gidansa, an kuma karbe makamai daga hannun masu tsaronsa.

Ana samu rashin jituwa a tsakanin shugaba kasar ta Saliyo da kuma mataimakinsa.

A kwanannan aka kore shi daga jam'iyyar da ke mulkin kasar inda ake zarginsa da yaudara da zamba da kuma ta da rikici, zargin da ya musanta.