Za mu kawar da 'yan ta'adda — Shugaban Tunisia

Hakkin mallakar hoto
Image caption Duniya na Allawadai da harin ta'addanci a Tunisia

Shugaban kasar Tunisia, Beji Ceid Essebsi ya sha alwashin fuskantar kawar da ta'addanci daga kasar bayan harin da aka kai a kasar.

Mr Essebsi, wanda ya yi bayani ga 'yan kasar ta gidan talabijin cikin kakkausar murya, ya lashi takobin kawo karshen wadanda suka kai hari a kan gidan adana kayan tarihi a Tunis ranar Laraba.

Ya ce "Ina son al'ummar Tunisiya su fahimci cewa muna fuskantar barazanar yaki daga 'yan ta'adda. Ba za mu yarda wadannan tsirarun mutanen masu kishin jinin mutane su sanya mana firgici ba, za mu sa-kafar-wando-daya da su har sai mun ga bayan su ba tare da tausaya musu ba".

Harin dai na ci gaba da shan suka daga kasashen duniya da daidaikun mutane.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce aikin 'yan ta'adda ba zai sauya alkiblar kasar Tunisia daga turbar dimokradiyya ba.

Babban Sakataren Majalisar, Banki-Moon da shugaban Amurka Barack Obama su ma sun soki al'amarin.

Harin dai na ranar Laraba yayi sanadiyyar mutuwar mutane 19 da suka hada da 'yan yawon bude ido guda 17 da kasashen Japan da Italy da Columbia da Spaniya da Faransa da kuma Australia da Poland, ya kuma jikkata mutane 40.