Amurka ta kashe jagoran al-shabaab

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan al-shabab sun addabi kasashen Kenya da Somalia

Hukumar tsaro ta Pentagon ta ce ta kashe jagoran kungiyar mayakan al-shabab ta Somalia, a wani hari da aka kai masa da jirgi marar matuki.

Jami'an sojin tsaron Amurka, sun ce an kashe Adnan Garar a kudancin Somalia a ranar Juma'ar da ta gabata, kuma shi ne mutumin da ake zargi da shirya hari a kan rukunin shagunan Kenya shekaru biyu da suka gabata.

Amurka dai ta yi ta nazarin farmakin kafin tabbatar da cewa Gararr ake kashe.

Ta kuma hari wasu jigogi a kungiyar ta hanyar amfani da wadannan jiragen marasa matuka, da suka hada da tsohon jagoran kungiyar Ahmed Godane.