2015: Amurka za ta taimaka wa Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption mataimakin shugaban Amurka, Joe BIden

Amurka ta ce za ta taimaka wa Najeriya wajen ganin an gudanar sahihin zabe kuma cikin lumana.

Mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden ne ya bayar da tabbacin a wata tattaunawa da ya yi ta waya da shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta APC, Janar Muhammad Buhari ranar Laraba.

Mista Biden ya jinjinawa shugaba Jonathan da Janar Buharin bisa rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi a watan Janairu domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ba.

Sai dai mataimakin shugaban kasar Amurkan ya kara da nuna damuwarsa dangane da tashin hankali da aka samu a kasar a lokutan kamfe, a inda ya kara tunatar da 'yan takarar bukatar da ke akwai ta yin siyasa ba da gaba ba.

Daga karshe, Mista Biden ya ce kasar Amurka tana maraba da sahihin zabe wanda kuma ba bu tashin hankali a cikinsa, sannan Amurkar zata ci gaba da kasancewa tare da Najeriyar a kowane irin yanayi.