'Yan Boko Haram sun sake kai hari Gamborou

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Kasuwar Gamboru da 'yan Boko Haram suka kona a bara

Rahotanni daga Gamborou da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru sun ce 'yan Boko Haram sun koma cikin garin inda suka kona gidaje da dama.

Bayanai sun ce mayakan Boko Haram sun samu sukunin koma wa garin ne saboda babu isassun jami'an tsaron Nigeria a garin tun bayan da dakarun Chadi suka kwato garin daga hannun masu ikirarin jihadi.

Wani mazaunin garin Gamborou ya shaida wa BBC cewa mayakan Boko Haram din sun yi barna sosai, kuma kafin wannan harin sun yi ta dauki daya-daya na kisan mutane.

A farkon watan Fabarairu ne dakarun Chadi suka kwace garin Gamboru daga hannun mayakan Boko Haram.

Dakarun Najeriya tare da hadin gwiwar na Chadi da Kamaru da kuma Nijar sun kaddamar da yaki a kan Boko Haram inda bisa dukan alamu a yanzu suke samun nasara a kan mayakan.