Shin ‘yan Biritaniya na da ‘yanci kan wariyar launin fata?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jam’iyyar UKIP na son ta rage yawan ‘yan ci-rani

Al’umma ce wacce ta hada kabilu kabilu daban-daban, amma shin mutanen Biritaniya na sake wa wajen tofa albarkacin bakinsu a kan al’amuran da suka shafi mutane ruwa biyu da kuma batun kabilanci ko harshe?

A wani shirin talbijin, shugaban wata kungiya mai sa ido don samun daidaito tsakanin kabilu a Biritaniya, Trevor Phillips, ya lissafo korafe-korafe masu cike da cece-kuce.

Wanda yafi shahara kuwa shi ne kokarin girmama ‘yan kabilu marasa rinjaye da kawar da wariyar launin fata, wadanda suke sanya mutane tsoron tattauna al’amura masu muhimmanci don ka da a kaga musu adawa kasancewarsu ‘yan tsirari.

Wakilin BBC kan zamantakewar al;umma John McManus ya fayyace wannan zazzafar muhawara ta Biritaniya.

A matsayinsa na wanda ke shugabantar hukumar tabbatar da daidaito tsakanin kabilu,

tun shekaru 10 da suka wuce, Trevor Phillips yana barin ofishinsa da ke London na ‘yan kwanaki a duk mako don ganawa da al’ummomin kabilu marasa rinjaye a gaba daya kasar.

Mr Trevor wanda asalinsa bakar fata ne ‘yan cirani, ya jaddada bukatar kawo daidato a cikin al’ummar da ke da mabanbantan ra’ayoyi.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jeremy Clarkson- shi yana nuna wariya ne ko kuma yana bayyana ra’ayinsa ne

A cewarsa akwai wasu kungiyoyi da ya sani suna ruruwa kiyayya.

A shirin Tabalijin din, Mr Phillip ya ce akwai matsaloli biyu, watakila na farko shi ne ba a son a tattauna batun a tsakanin al’umma ko kuma ba a daukar matakan magance matsalar.

To amma me yasa bai fasa kwoi ba?

A cewar jam’iyyar UKIP na samun farin jini a Biritaniya ne saboda akidarta na takaita shigowar ‘yan ci-rani kuma kasar ta fita daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Nuna rashin adalci

Ana fuskantar matsalar yin lalata da kuma cin zarafi daga wajen al’ummomi, inda a Rotherham, wasu mutane ‘yan asalin Pakistan ke lalata da ‘yan mata kananana kuma hukumomi suka kawarda kai saboda fargabar ka da a ce suna nuna wariyar launin fata.

A makon da ya gabata a Biritaniya, an dakatar da wani shararren ma’aikacin BBC saboda ya nushi abokin aikinsa lamarin da ya janyo cece-kuce a shafukan zumunta na zamani.

A yanzu ana tuhumar Jeremy Clarkson mai gabatar da shirin Top Gear da laifin cin zarafi.

A baya an gargadi Mr Clarkson saboda amfani da wasu kalamai na nuna wariya a kan ‘yan asalin nahiyar Asiya.

A baya can a shekara ta 2005 ne wasu masu kishin islama haifaffun Biritaniya suka kai harin bama-bamai London, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 52 da yawa kuma suka jikkata.