'Yan matan Chibok su na raye-Jonathan

Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya,Goodluck Jonathan ya ce ya yi imanin cewa 'yan matan nan sama da 200 da aka sace daga garin Chibok suna raye kuma za su ceto su.

Bayanin kuwa yana zuwa ne kwanaki kadan bayan da rundunar sojin kasar ta ce ba ta da masaniyar inda 'yan matan suke.

Jonathan ya kara da cewa da farko gwamnatinsa ta raina irin karfin da kungiyar Boko Haram take da shi, hakan ne ma yasa har 'yan kungiyar suka samu damar kame wasu garuruwa, suka kuma ayyana su a matsayin daulolinsu.

Kan halin da ake ciki yanzu dangane da yakin da sojojin kasar suke yi da kungiyar ta Boko Haram, mista Jonathan ya ce a har kullum karfin 'yan Boko Haram kara karewa yake yi. Kuma yana fatan nan da wata daya za a kammala fatattakarsu.