Boko Haram: Nijar na fuskantar rashin abinci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijira ne ke samun mafaka a Jamhuriyar Nijar

Jamhuriyar Nijar ta ce kwararar da 'yan gudun hijira daga Najeriya ke yi cikinta za ta ta'azza mummunan halin da 'yan kasar ta ke ciki na rashin abinci.

Kasar dai ta fada cikin matsalar yunwa a shekarun da suka wuce, amma a wannan shekarar lamarin ya karu sakamakon shigar dubban 'yan gudun hijirar da suka tsere wa tashin hankali saboda hare-haren 'yan Boko Haram.

Ofishin da ke bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya kiyasta cewa mutane miliyan uku da dubu dari hudu ne uke fama da rashin abinci a kasar.

'Yan kungiyar Boko Haram dai sun kai hare-hare a kasar ta jamhuriyar Nijar, da Kamaru da Chadi, baya ga hare-haren da suke kai wa a Najeriya.