Boko Haram: Da sauran rina a kaba-Rahoto

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram za su ci gaba da kai hare-haren sari-ka-noke

Wani rahoto na musamman da gamayyar kwararru kan tsaro ta Nigeria Security Network ta fitar ya ce duk da cewa gwamnatin Najeriya tana samun galaba akan Boko Haram, hakan ba ya nufin an kawo karshen yaki da ta'addanci.

Duk da cewa rahoton ya yi la'akari da kokarin sojojin kasar na kwato garuruwa daga hannun Boko Haram, to amma fa ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba domin 'yan ta'addar za su ci gaba da kaddamar da hare-haren sari-ka-noke.

Rahoton kuma ya bayyana takaicinsa bisa wani rahoton da ba a tabbatar da sahihancinsa ba da ke nuna cewa ana amfani da sojojin kasashen waje a yakin da ake yi da Boko Haram din.

Idan dai har hakan ya tabbata, kamar yadda rahoton ya ce to ba bu abin da al'amarin zai haifar illa ya kara wa al'ummar yankunan karin kin jinin kasashen yammacin duniya sannan kuma zuciyarsu ta karkata ga Boko Haram.

Rahoton dai ya ce yin amfani da sojojin kasashen wajen a yankunan ka iya haifar da keta haddin bil'adama.