Jonathan ya je yakin neman zabe a Yobe

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Mr Jonathan na fuskantar kalubale daga wajen Janar Buhari na APC

Rahotanni daga Damaturu babban birnin jihar Yobe na cewa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyarar yakin neman zabe a jihar.

A baya dai an shirya shugaban zai kai ziyarar yakin neman zabe a jihar, amma aka dage saboda dalilai na tsaro, kafin daga bisani a jinkirta zaben kasar daga watan Fabarairu zuwa Maris.

Jihar yoben na daga cikin jihohi uku da suka fi fuskantar hare-haren yan kungiyar Boko Haram.

A baya-bayan nan dai hukumomin sojin Najeriya sun sanar da cewa sun kwato dukkan yankunan jihar Yoben da ke hannun yan kungiyar Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane fiye da 13,000 a cikin shekaru shida a Najeriya.