An kama mutane kan kona Qur'ani a Afghanistan

'Yan sandan kasar Afghanistan sun kama mutane hudu dangane da kisan da aka yi wa wata mata da aka zarga da kona Al-qur'ani a cikin wani masallaci.

Wadansu mutane ne suka fito da ita daga wani masallacin birnin Kabul da karfin gaske, suka lakada mata duka, kuma suka kona ta.

'Yan uwanta sun ce da ma can tana fama da ciwon tabin hankali.

Ana kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da wulakanta Al-Qur'ani da aibunta Annabi Muhammad (SAW) a Pakistan, sai dai ba a cika samun hakan a Afghanistan ba.