Facebook: An kama mai karyar shirin kashe kansa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Facebook ya rufe shafin mutumin

An kama wani mutum da ya rubuta cewa yana shirin kashe kansa a shafin Facebook aka kuma tura shi gidan masu tabin hankali tsawon kwana uku.

Shane Tusch mai shekara 48, wanda mai aikin lantarki ne a San Mateo da ke California, a Amurka, ya ce ya yi hakan ne domin jarraba tsarin Facebook na kare aikata kashe kai.

Bayan da ya rubuta a shafinsa na Facebook ne yana shirin rataye kansa a gadar Golden Gate Bridge, wani da ya karanta sakon ya sanar da 'yan sanda, su kuma suka je suka kama shi.

Mr Tusch ya yi korafin cewa, ba a ba shi kulawar da ta dace ba a inda aka tsare shi, sai dai kawai an yi ta jarraba lafiyarsa.

Hakkin mallakar hoto facebook.com
Image caption Yarinya 'yar shekara 16 da ta kashe kanta a Sri Lanka bayan da hotonta da na saurayinta ya bayyana a Facebook

A watan Fabrairu masu gudanar da shafin na Facebook, suka fadada tsarin shafin na kare aikata kashe kai, inda suka bayar da dama ga duk wanda ya ga wani na son kashe kansa ya nuna, domin a kare aikata hakan.

Da zarar an sanar da Facebook, masu shafin za su tuntubi mutumin da ke son kashe kan nasa, su yi mi shi tayin taimako.

Idan kuma abin ya fi karfin haka, masu shafin sai su sheda wa 'yan sanda domin su gudanar da bincike.

Mr Tusch, wanda yake da aure da 'ya'ya biyu, ya ce, abin da ya gano bayan da aka tsare shi, ya fallasa wahala ko hadarin da ke tattare da tsarin kariyar na Facebook.

Ya ce, ya yi hakan ne kawai domin ya jarraba tsarin taimkon na Facebook, wanda yanzu ya gano matsalar da ke tattare da shi.