Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tsaro a lokacin zabe

Hukumar zaben Najeria, INEC, ta ce a shirye ta ke domin gudanar da zaben kasar da za a fara ranar 28 ga wannan watan.

Sai dai wasu na nuna damuwa akan maganar tsaro lokacin zaben, musan ma a wassu jihohin kasar.

Har yanzu dakarun Najeriya tare da taimakon rundunar hadin gwiwa ta kasa-da-kasa na kokarin kwace sauran garuruwan da suka saura a hannun 'yan Boko Haram.

Wane tanadi hukumomin tsaro suka yi don ganin cewa ba a samu tashin hankali ba?

Menene matsayin yankunan da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram lokacin zaben?