'Wasu 'yan PDP na kyamar hoton Jonathan'

Hakkin mallakar hoto AFP

A Nigeria wasu kungiyoyi da ke yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan sun koka bisa yadda wasu 'yan takara a jam'iyyar ba sa hada hotunansu da nasa.

A cewar masu irin wannan ra'ayi dai ya kamata kowanne dan takara ya yi wa jam'iyyarsa fafutuka, ba kawai ya yi wa kansa ba.

A jihar Kano dai lamarin ya kai ga zarge-zargen bata suna tsakanin 'yan PDP da APC a wasu yankunan.

To sai dai wasu shugabannin PDP na cewa rashin hada hotunan ba shi da wata illa.