Jirgin kasa ya kashe mutane 30 a India

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani jirgin kasa ya kauce daga kan layin dogo a kasar India, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 30.

Al'amarin ya faru ne a Jihar Uttar Pradesh.

Jirgin, mai suna Janta Express, wanda ke tafiya a tsakanin garin Dehradun da Varanasi, ya samu matsala ne a wani kauye mai suna Bachhrawan.

Mutane da yawa sun jikkata a wannan hadari, kuma an dauki hotuna da dama da suka nuna yadda jirgin ya kauce daga layin dogon.

Karamin ministan ma'aikatar jirgin kasa, Manoj Sinha, ya ce an fara gudanar da bincike a kan abin da ya janyo hadarin.