Amurka na tsaurara tsaro a Niger da Mali

Hakkin mallakar hoto
Image caption Amurka ta dauki matakin ne domin hana 'yan ta'adda kai musu hari.

Ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali sun kara yawan dakarun da ke tsaron jami'ansu a kasashen.

A wata sanarwa da jami'an ofisoshin suka fitar sun ce sun tsaurara tsaro a ofisoshi da kuma iyalan jakadunsu da ke kasashen biyu.

A cewarsu, an dauki matakin ne domin hana kai musu hare-hare, musamman daga kungiyoyin da ke da tsattsauran ra'ayi.

A Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, a ranar Alhamis ne aka kara yawan jami'an tsaron da ke gadin makarantun da 'ya'yan jakadun Amurka ke zuwa.