'Yan bindiga sun sace sarkin Bukuyum

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Hukumomin jihar sun ce, 'yan sanda na ci gaba da daukar matakan gano inda aka nufa da sarkin

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace sarkin Bukkuyum, da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya, mai martaba Alhaji MUhammadu Usman.

'Yan bindigar da suka kama sarkin a masallacin kofar gidansa,ranar Juma'a bayan sallar Magriba kafin Isha'i, sun yi harbe-harbe na tsorata jama'a kafin su yi awon gaba da sarkin a wata mota da suka zo da ita.

'Yan bindigar sun kuma kwace wayoyin mutane da ke masallacin a lokacin harin, kamar yadda kwamishinan watsa labarai na jihar ta Zamfara, Alhaji Ibrahim Magaji, ya tabbatar wa BBC.

Wasu rahotanni sun ce lamarin ya faru ne kwana daya bayan da sarkin (mai daraja ta daya) ya nuna goyon bayansa ga gwamnan jihar Alhaji Abdul'Aziz Abubakar Yari Gandi, wanda ke neman zabe a karo na biyu.