Gwamnati za ta kama jagororinmu-APC

Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Sai dai PDP ta kalubalanci APC ta kawo shedar zargin

Babbar jam'iyyar hamayya ta APC a Najeriya ta yi zargin gwamnatin PDP da wani yunkurin kame jiga-jiganta domin kassarata a zabukan da ke tafe.

Jam'iyyar ta yi wannan zargi ne yayin da ya rage saura kwanaki shida a fara zabukan kasar.

Jam'iyyar ta APC ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta kira a Lagos.

Mai magana da yawun jam'iyyar ta APC Alhaji Lai Muhammad ya ce, gwamnatin PDP na shirin kama jagororinsu ba Bola Ahmed Tinubu kadai ba, har ma duk wani da take ganin yana sama musu kudade.

Haka kuma za a gurfanar da su a gaban shari'a kafin zaben na ranar Asabar

Sai dai mataimakin kakakin jami'iyyar PDP, Barrister Ibrahim Jallo, ya musanta zargin da cewa shaci-fadi ne da kuma yarfe, abin da ba za ka raba harkar siyasa da shi ba.