An gano katon rami da gawarwaki a Borno

Katon ramo da gawarwaki a Borno
Image caption Katon ramo da gawarwaki a Borno

An gano gwarwakin mutane akalla 70,a garin Damasak da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, bayan da aka kwato garin daga mayakan kungiyar Boko Haram.

Dakarun Jamhuriyar Nijar da na Chadi ne suka bayar da wannan sanarwa ta cewa sun gano wani makeken rami da aka binne gawarwakin mutanen a kusa da garin Damasak a jihar ta Borno.

Garin na Damasak mai iyaka da kasar Nijar ya kasance a hannuwan 'yan kungiyar Boko Haram kafin sojojin kasashen su kwato shi.

Alamu dai sun nuna an kashe mutanen ne da dan jimawa ganin yadda, iskar hamada ta fara busar da gawarwakin.

Wasu daga cikin mutanen an yi musu yankan rago, daya ma har an cire masa kai.

Karin bayani