Shawarwari kan shirin nukiliyar Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Iran Hassan Rouhani

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani yace cigaban da aka samu na baya bayan nan za su iya kaiwa ga cimma yarjejeniya game da shirin nukiliyar kasar

Yayinda wa'adin da aka sanya domin cimma yarjejeniyar ke kara karatowa kasashe masu ruwa da tsaki a tattaunawar sun ce suna da kwarin giwa za'a cimma masalaha.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace an sami cigaba mai ma'ana ko da yake har yanzu akwai sauran gibin da ba'a cike ba.

" Yace za mu tsara hade dabarun mu yayin da muke tunkarar karshen wa'adin watan Maris domin cimma fahimtar juna akan muhimman batutuwa".