Monica Lewinsky ta nemi da a rika nuna tausayi a Intanet

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption ''An kira ni da sunaye na batanci daban-daban, har na kusa rasa raina'' in ji Monica Lewinsky

Tsohuwar mai neman sanin makamar aiki a fadar Amurka ta White House, Monica Lewinsky, wadda labarin soyayyarta da Shugaba Clinton ya karade duniya a 1998 ta yi kira da a rika nuna tausayi a sakonnin da ake sa wa a intanet.

Ms Lewinsky ta gabatar da jawabi ne a wani taro kan al'amuran da suka shafi fasaha da nishadi da kuma zayyana, da ake wa lakabi da TED, a takaice.

Matar ta bayyana kanta a matsayin daya daga cikin, wadanda aka ci zali ta intanet, lamarin da a yanzu ta ce ya zama ruwan dare, inda mutane ke jin dadin kallon sirri ko abin kunyar da wasu suka aikata ta intanet.

Wannan shi ne karo na biyu da Monica Lewinsky ta fito bainar jama'a ta yi jawabi, tun lokacin da aka daina jin duriyarta a 2005, bayan da a watan Oktoba ta yi jawabi a babban taron Forbes na 'yan kasa da shekara 30.

Matar ta fara jawabinta ne da barkwancin cewa, ita kadai ce wadda take shekara arba'in da wani abu da ba ta fatan ta sake dawo wa 'yar shekara 22.

Ta ce, ''ina 'yar shekara 22 na shiga soyayya da shugabana. A shekara 24 na gane kuskuren hakan.''

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Wani hoto na Shugaba Clinton da Ms Lewinsky

Batun badalar da ke tsakanin Shugaba Bill Clinton da Monica Lewinsky na daya daga cikin manyan labaran da suka bazu ta intanet a duniya.

Ms Lewinsky ta ce, intanet ta kara munin abin kunyar da ta yi, inda a 1998, lamarin ya zama na dambarwar siyasa da shari'a da kuma na kafofin yada labarai, yadda ba a taba ganin kamarsa ba a baya.

Kuma ta ce ci gaban da aka samu ta hanyoyin sadarwa, shi ne ya kawo hakan.

Ms Lewinsky ta kara da cewa, ''a wannan lokacin, na zama daga matar da ba wanda ya sani zuwa wadda duniya ta san ta, ta ko ina sai gungun jama'a ne ke jifa na.''

''An kira ni da suna na batanci daban-daban, kamar karuwa da sakarya da fitsararriya da makamantansu.

Na rasa mutuncina da kima kai na ma kusa rasa raina.''