Dakarun Chadi sun sake komawa Gamboru

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga jihar Borno a arewacin Najeriya sun ce dakarun kasar Chadi sun sake shiga garin Gamboru Ngala wanda ke iyakar Najeriya da Kamaru.

Sun shiga ne bayan da 'yan Boko Haram suka sake kai hari a garin, inda suka kashe mutane da dama.

A makonnin baya ne dakarun Chadin da na Kamaru suka kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram. Bayan sun tafi ne wasu 'yan Boko Haram din suka koma suna kai hari.

Hukumomin Najeriya ba su tura sojojinsu zuwa garin ba bayan fitar dakarun Chadin -- abin da mutanen yankin suka ce ya haddasa dawowar 'yan Boko Haram.

Wata mata 'yar garin ta gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa 'yan Boko Haram din sun kashe fiye da mutane talatin a hare-haren da suka kai.

Matar, wadda a halin yanzu ta ke a garin Fotokol na Kamaru, ta ce hare-haren sun tilasta wa mutane sake tserewa.

Amma ta ce a ranar Asabar dakarun Chadin sun sake komawa Gamboru Ngalan. An ga manyan motocin sojin Chadi suna shiga garin.

Wasu rahotanni sun nuna cewa 'yan Boko Haram din sun tsere kafin shigar dakarun.

Karin bayani