Boko Haram:Sojin Najeriya sun nuna damuwa

Image caption Sojojin Najeriya sun ce ana son bata musu suna ne kawai

Rundunar Sojan Nijeriya ta nuna bacin ranta ga abinda ta kira wata jita-jita maras tushe da ake yadawa ta kafofin watsa labarai na waje game da matakan da rundunar hadin-gwiwa ta kasashen Yammacin Afrika ke dauka na yaki da 'yan Boko Haram.

Cikin wata sanarwa da aka buga a wata kafar watsa labarai ta internet da ake kira PRNigeria, rundunar sojan Nijeriyar ta ce, babu kanshin gaskiya a jita-jitar da ake yadawa cewar sojojin kasar sun ki karbar wasu yankuna da dakarun rundunar hadin-gwiwa suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.

A martanin da ya mayar kan batun Daraktan watsa labarai na ma'aikatar tsaron Nijeriya Manjo Janar Chris Olukolade ya musanta cewar sojojin Nijeriyar sun ki karbar yankunan da dakarun rundunar kawancen suka kwato daga Boko Haram.

Rundunar Sojan Nijeriyar dai tana mai da martani ne a kan wani rahoto da aka bayyana cewar Jaridar New York Times ta buga a ranar Jumma'a wanda ya ambata cewar Sojojin kasashen waje sun roki sojojin Nijeriya su karbi garuruwan da aka kwato daga kungiyar.

Jaridar tace, dakarun na kasashen waje sun jagoranci 'yan jarida ne a wani rangadi na aiki cikin garuruwan da aka kwato daga Boko Haram, wuraren da babu duriyar sojojin Nijeriya.

Ma'aikatar tsaron Nijeriyar ta ce a kai-a kai a kan dangana wasu kalamai na cin fuska daga wasu jami'ai da ba a ambaci sunansu ba daga kasashe makwabta renon Faransa na rundunar kawance, don dai kawai dakushe kimar Nijeriya tare da muzanta sojojinta.