Biyan manoma ta Internet yana da matsala

Manoma Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manoma

An yi watsi da wani tsari na miliyoyin fama-famai a Ingila na biyan manoman Tarayyar Turai tallafi saboda matsalolin dake tattare da tsarin.

Za a sake kaddamar da shirin a mako mai zuwa bayan da aka nemi manoma su gabatar da lissafin hakkokin da suke bi a rubuce kan takarda.

Manoman sun ce, sun sha gwagwarmaya da shafin wata da watanni a kokarin da suke yi na neman biyan wasu hakkokin su.

Mark Grimshaw babban jami'in hukumar biyan manoman karkara da ake kira Defra RPA ya ce an yanke shawarar ne bayan an saurari koke-konen manoman.

Ya bayar da sanarwa ne a wani shiri na BBC radio 4 - shirin manoma a yau.

Grimshaw din ya kara da cewa, Defra ta yanke shawarar tabbatar da cewa dukkan wanda yake son neman hakkinsa a wannan shekarar zai iya yi.

Wannan shiri na BPS shine babban shirin tallafi ga manoma ana Tarayyar Turai.

Hukumar ta Defra ta ce, za a cigaba da rajistar wani bangare na tsarin a wannan shekarar. Daga nan sai, hukumar ta dora bayanan a shafin internet.

Sai dai kuma an maye gurbin tsarin daukar zayyanar iyakokin gonaki wanda shine ke haddasa babbar matsalar, da tsarin daukar hoton a kan takarda.

Manoma da wakilansu za su iya samun tallafin a cibiyoyin bayar da tallafi 50 a Ingila wadanda a yanzu za su zamo ciboyiyin da manoma za su iya zuwa a kodawane lokaci.

Karin bayani