Ana neman 'yan Kamarun da aka sace

Hakkin mallakar hoto .

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru na can na neman bayanai kan mutane 16 da aka sace a kasar.

Daga cikin wadanda aka sacen har da wasu masu unguwanni na garin Lagdo da ke arewacin kasar.

A ranar Juma'a ne aka sace mutanen suna cikin motar fasinja a kusa da garin Garoua-Boulai ta gabashin kasar.

Wasu mutanen da ba'a tantance ba ne suka yi awon gaba dasu a lokacin da suke cikin karamar motar hayan, kirar Hiace.

An sace su ne a kan hanyarsu ta komawa garinsu Lagdo sa'adda suke dawowa daga wurin jana'iza a wani kauye a gabashin kasar.

Wasu mazauna garin Lagdon sun gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa suna cikin bakin ciki sosai akan wannan lamari.

Karin bayani