An ba Rajendra Singh lambar yabo ta ruwa

Sanar da ruwa mai tsafta ga al'umma Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sanar da ruwa mai tsafta ga al'umma

An bayar da wata kyauta yabo wadda aka yi ma lakani da "kyautar yabo ta ruwa" ga wani dan kasar India mai fafutuka wanda ya samar da ruwan sha mai tsafta ga Kauyuka 1,000.

Alkalai a wurin bayar da kyautar a Stockholm ya ce hanyoyin da mutumen ya bi har ila yau kuma sun kare samun ambaliyar ruwa tare da farfado da kasa da koguna tare da maido damun daji.

Rajendra Singh wanda ya smu kyautar, an kira shi "mutumen ruwa na India".

Alkalan suka ce dabarun da ya yi aiki da su, masu sauki ne kuma da rahusa, ya kamata kuma a rinka bin wannan hanyar a dukkan fadin duniya.

Mr Singh ya yi amfani da salo na zamani na hanyoyin da na tara ruwan sama.

Dabarun sun kunshi gina kananan madatsun ruwa, domin datse ruwan daga gangarewa a lokacin damuna tare da barin kasa ta tsotse shi don amfani da shi a gaba.

Ya samu horo ne a fannin sha'anin kiwon lafiya, to amma lokacinda ya samu aiki a yankin karkara a Rajasthan, an sheida masa cewar matsalar da ake da ita, ta ruwan sha ce, ba ta kiwon lafiya ba.

Manoma sun tsotse ruwan dake kasa kuma yayinda ruwan ya kafe, tsirrai da koguna suka bushe, namun daji suka gudu, mutane suna kwarara cikin garuruwa.

Mr Singh yace, "a lokacinda muka fara aikinmu, muna neman kawar da matsalar ruwan sha ne kawai.

"A yau, burin da muke da shi mai girma ne. Wannan wani karni ne na duba hanyoyi da nazarin gurbatar muhalli da kwararar hamada. Domin dakatar da duk wadannan, domin ci yaki na kawar da matsalar ruwa, wannan shine buri na a rayuwa" - in ji Mr Singh.

Karin bayani