Babu isasshen ruwa mai kyau a Nijeriya - UNICEF

Wata Mata tana dibar ruwan sha a rafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wata Mata tana dibar ruwan sha a rafi

Yau ce Ranar Ruwa ta Duniya, wacce Majalisar Dinkin Duniya ta ware don wayar da kan jama'a kan muhimmancin tsaftataccen ruwa.

A cewar majalisar ta dinkin duniya dai, tsaftattaccen ruwa ne kashin-bayan ci gaban al'umma; kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa jin dadin al'umma.

Rana ce kuma ta tunawa da al'ummomin da ke fama da matsalar ruwa.

A cewar asusun kula da kananan yara na Majalisar ta Dinkin Duniya, UNICEF, mutane kusan miliyan 70 ne ba su samun tsaftataccen ruwa a Najeriya, yayinda wasu miliyan 110 ba su da tsaftataccen muhalli.

Karin bayani