Sauyin yanayi zai yi ma China babbar illa

Sauyin yanayi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sauyin yanayi

Babban masanin kimiyya na China yai kashedi a wata sanarwa da hukuma da ba kasafai a kan yi irin ta ba cewar, Sauyin yanayi, zai iya haddasa babbar illa ga China, abinda zai kawo raguwar abincin da aka noma da kuma yin illa ga muhalli.

Zheng Guogang ya gaya ma kamfanin dillancin labarai na China Xinhua cewar sauyin yanayin zai iya haifar da mummunar illa ga manyan ayyuka a China.

Yace, ma'aunin yanayi ya nuna sauyin yanayin ya rigaya ya zarce kimar da aka yi ta kasashen duniya.

Kasar ta China wadda ita ce kan gaba wajen gurbata muhalli ta ce, hayakin da kamfanonin ta ke fitarwa za su kai kololuwa zuwa shekara ta 2030.

Sai dai kuma, kasar ba ta tsaida wani kuduri ba a kan rage yawan hayakin.

Mr Zheng wanda shine Shugaban hukumar nazarin yanayi ta kasar ya ce yanayi mai zafi ya jefa kasar sa cikin wani hadari na samun sauyin yanayi da kuma bala'in yanayi.

Yace, yanayin mai zafi a China ya rigaya ya kai makura fiye da kiimar da aka yi a duniya tun a karnin da ya gabata.

Michael Bristow mai sharhi kan al'amurran yankin Asia a BBC ya fada cewar wannan sanarwa ba kasafai wani babban jami'in gwamnati ya kan yi irin ta ba a China.

Shugabannin Chinar dai sun amsa cewar akwai illa dake tattare da sauyin yanayin a duniya, to amma yawanci ba su nuna irin mtsalolin da hakan zai hadda.

Karin bayani