Kwalara ta kashe 121 a Ghana

Image caption Rashin tsaftataccen ruwa na cikin abubuwan da ke kawo cutar

Hukumomi a kasar Ghana sun ce cutar amai da gudawa ta kashe kimanin mutane 121 a Accra, babban birnin kasar tsakanin watan Yunin shekarar 2014 zuwa watan Fabrairun shekarar 2015.

Hukumomin lafiyar kasar sun ce a cikin lokacin fiye da mutane 20, 000 ne suka kamu da cutar.

Sun kara da cewa wannan shi ne karon farko da aka samu wannan adadi na mutanen da suka kamu da ita a tarihin kasar.

Rashin tsafta da rashin tsaftataccen ruwa na cikin abubuwan da ke kawo cutar ta amai da gudawa.