Dalilin da ya sa ban halarci muhawara ba — Buhari

Janar Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Janar Muhammadu Buhari ya ce ba ya tsoron yin muhawara.

Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar APC, Janar muhammadu Buhari, ya ce bai halarci muhawara da shugaba Goodluck Jonathan ba saboda yunkurin da ake yi na bata masa suna.

Da yake bayani a kan dalilan Janar Buhari na kin halartar muhawarar, daraktan kwamitin watsa labaransa, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa wadanda suka shirya muhawarar magoya bayan Mr Jonathan ne, domin haka ya san ba za su yi wa dan takarar APC adalci ba.

Ya kara da cewa Janar Buhari ba ya jin tsoron yin muhawara, yana mai cewa tun da ya fara takara a shekarar 2003 dukkanin 'yan takarar da ke hamayya da shi sun ki halartar muhawara da shi.

A cewarsa, shi ma yanzu ba shi da lokacin tsaya wa da su.

'Yan takara sun yi muhawara

Koda yake Janar Buhari bai halarci wajen muhawarar ba, amma wasu daga cikin 'yan takarar shugaban kasar sun halarta, inda suka bayyana manufofin jam'iyyunsu.

A wajen mahawarar, 'yan takarar da suka hada da Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP, sun sha alwashin magance matsalolin kasar idan aka zabe su.

Karin bayani