Jagoran Singapore Lee Kuan Yew ya mutu

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Lee Kuan Yew ne ya sauya kasar ta Singapore

Dattijon da ya kawo sauye-sauye a kasar Singapore, Lee Kuan Yew, ya mutu yana da shekaru 91 a duniya.

Za a yi masa jana'izar girmamawa ranar 29 ga watan Maris, bayan an kwashe mako guda ana yin makoki.

Lee Kuan Yew, wanda ya rike mukamin Firai Ministan tsawon shekaru 31, shi ne mutumin da ya sauya kasar daga kasancewarta 'yar karamar kasa zuwa kasa mai bunkasar tattalin arziki da ke gogayya da manyan kasashen duniya.

Sai dai ya sha suka daga wasu 'yan kasar bisa kin barin mulki da wuri.

A karkashin mulkinsa, an tauye hakkin mutane na fadar albarkacin bakinsu, kuma 'yan hamayya sun sha dauri.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin din kasar, Firai Minista Lee Hsien Loong ya ce, Mr Yew ne ya yi fafutikar sama wa kasar mulkin-kai.

Ya ce, "Ya yi fafutikar sama wa kasarmu 'yancin kai, sannan ya gina ta, shi mutum ne da duk dan kasar Singapore ke alfahari da shi."