Za a magance Ebola a watan Agusta

Yaki da cutar Ebola Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cutar Ebola ta kashe mutane da dama

Shugaban shirin yaki da cutar Ebola na Majalisar Dinkin duniya, Ismael Ould Sheik, ya ce yana sa ran a kawo karshen barkewar annobar a yankin Afrika ta yamma zuwa karshen watan Agusta.

Mr Ould Sheik ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, yayin cika shekara daya da bullar annobar, wadda ta hallaka mutane sama da dubu goma.

Akasarin mutane da cutar ta kashe sun fito ne daga kasashen Guinea da Saliyo da kuma Liberia.

A tattaunawar da BBC ta yi da kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya, MSF ta ce babu wani gaggarumin ci gaba da aka samu na raguwar mutanen da ke kamuwa da annobar tun watan Janairu.

Karin bayani