Wani jirgi ya yi hatsari a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin na dauke ne da mutane 144

Wani jirgin sama samfurin Airbus A320 ya yi hatsari a kudancin kasar Faransa.

Wani gidan jirida a yankin na Alps ta bayyana cewar jirgin na dauke da fasinjoji 144 da kuma ma'aikatansa guda shida.

Jirgin yana kan hanyarsa ne ta zuwa Duesseldorf daga Barcelone a lokacin da wannan lamari ya faru.

Jirgin, mallakar Germanwings ne, daya daga cikin reshen jiragen kamfanin Lufthansa na kasar Jamus.