A-320: Ana aikin gano gawarwaki mutanen da suka mutu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirage masu saukar angulu sun isa wurin domin ayyukan ceto

An komo da aikin binciken gawarwakin mutane 150 da suka mutu a hatsarin Jirgin saman Jamus da ya taso daga birnin Barcelona zuwa Duesseldorf.

Jami'ai sun ce za'a iya daukar kwanaki kafin a gano gawarwarkin mutanen da hatsarin Jirgin nan ya rusta da su a yankin Apls saboda rahin kyawun yanayi

Ana zaton babu wadanda suka rayu a cikin mutanen da suke cikin jirgin a lokacin da ya fadi.

Jami'in kamfanin jirgin ya bayyana cewar jirgin ya yi hatsarin ne a cikin minti takwas a kokarinsa na saukowa amma ba a sani ba ko ya nuna alamar matsala.

Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve ya ce masu aikin agaji sun gano na'urar nadar bayanan jirgin watau 'black box'.

An yi ammanar cewa akwai yaran makaranta 'yan Jamus su 16 da suka rasu a cikin jirgin.

Shugabanin Faransa da Jamus sun nuna kaduwa kan afkuwar wannan hatsari.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Markel ta shaida wa manema labarai cewa suna cikin jimami a wannan lokaci.

Ta kara da cewa ta na shirin ziyartar inda wannan hatsarin ya afku.

Rahotanni sun nuna cewa wani jirgin sama mai saukar angulu ya isa wurin mai cike da tsaunuka domin ayyukan ceto.