Isra'ila ta musanta zargin leken asiri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Netanyahu ya ce zargin ba shi da kanshin gaskiya.

Isra'ila ta musanta zargin da aka yi cewa ta yi leken asiri lokacin da manyan kasashen duniya, cikinsu har da Amurka, ke yin taro da Iran a kan makamashin nukiliyar Iran din.

Kakakin Firai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce zargin da jaridar Wall Street Journal ta yi musu a wani rahoto da ta buga, tsagwaron karya ce.

A cewarsa, jaridar ta yi zargin ne domin ta bata dangantakar da ke tsakanin Isra'ila da Amurka.

Jaridar dai ta ruwaito cewa Amurka ta gano Isra'ila tana leken asirin a lokacin taron da suke yi da Iran jim kadan bayan fara taron a shekarar 2014.

Wall Street Journal ta kara da cewa batun ya yi matukar batawa gwamnatin Amurka rai, musamman bayan ta gano cewa Isra'ila ta tseguntawa 'yan majalisar dokokin Amurka abin da ya wakana a lokacin taron.