Zabe: Ana kara fargabar barkewar rikici

Rikicin siyasa a Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin siyasa a Nijeriya

Yayinda zaben Nigeria ya ke kara karatowa, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda zaben zai kasance da kuma abin da ka iya biyo bayan zaben.

A yunkurin samar da zaman lafiya yayin zaben dai bangarori da dama na daukar matakai daban daban dan fadakar da mutane muhimmancin zaman lafiya da kuma illar tashin hankali.

Daga cikin masu fafutukar dai akwai majalisar mutane masu dabara ta Nigeria wato council of wise da ta hadar da wasu mashahuran mutane daga dukkan sassan Nigeria, wadanda suke kai ziyara jihohin kasar dan ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki musamman shugabannin al'umma kan anfanin zaman lafiya lokacin zabe.

Karin bayani